Saurari audio na Sheikh Ja’afar Mahmud Adam
عَنْ
أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ عَنْ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ:
"مَنْ نَفَّسَ عَنْ مُؤْمِنٍ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ الدُّنْيَا نَفَّسَ
اللَّهُ عَنْهُ كُرْبَةً مِنْ كُرَبِ يَوْمِ الْقِيَامَةِ، وَمَنْ يَسَّرَ عَلَى
مُعْسِرٍ، يَسَّرَ اللَّهُ عَلَيْهِ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ، وَمَنْ سَتَرَ
مُسْلِما سَتَرَهُ اللهُ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ ، وَاَللَّهُ فِي عَوْنِ
الْعَبْدِ مَا كَانَ الْعَبْدُ فِي عَوْنِ أَخِيهِ، وَمَنْ سَلَكَ طَرِيقًا
يَلْتَمِسُ فِيهِ عِلْمًا سَهَّلَ اللَّهُ لَهُ بِهِ طَرِيقًا إلَى الْجَنَّةِ،
وَمَا اجْتَمَعَ قَوْمٌ فِي بَيْتٍ مِنْ بُيُوتِ اللَّهِ يَتْلُونَ كِتَابَ
اللَّهِ، وَيَتَدَارَسُونَهُ فِيمَا بَيْنَهُمْ؛ إلَّا نَزَلَتْ عَلَيْهِمْ
السَّكِينَةُ، وَغَشِيَتْهُمْ الرَّحْمَةُ، وَ حَفَّتهُمُ المَلاَئِكَة،
وَذَكَرَهُمْ اللَّهُ فِيمَنْ عِنْدَهُ، وَمَنْ أَبَطْأَ بِهِ عَمَلُهُ لَمْ
يُسْرِعْ بِهِ نَسَبُهُ"
رَوَاهُ مُسْلِمٌ بهذا اللفظ
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him),
that the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) said:
Whoever removes a worldly grief from a believer, Allah will remove
from him one of the griefs of the Day of Resurrection. And whoever alleviates
the need of a needy person, Allah will alleviate his needs in this world and
the Hereafter. Whoever shields [or hides the misdeeds of] a Muslim, Allah will
shield him in this world and the Hereafter. And Allah will aid His slave so
long as he aids his brother. And whoever follows a path to seek knowledge
therein, Allah will make easy for him a path to Paradise. No people gather
together in one of the Houses of Allah, reciting the Book of Allah and studying
it among themselves, except that sakeenah (tranquility) descends upon them, and
mercy envelops them, and the angels surround them, and Allah mentions them
amongst those who are with Him. And whoever is slowed down by his actions, will
not be hastened forward by his lineage.
Related by (Muslim) in these words.
Transliteration
Daga Abu Hurairah Allah ya yarda da shi, daga Annabi (SAW) ya ce:
“Wanda duk ya kautarwa mumini wani baƙin ciki daga dangin baƙin
cikin da kan iya samun mutum nan duniya, To Ubangiji zai kautar masa da baƙin
ciki daga wani baƙin cikin da kan iya riskar bawa a gobe ƙiyama. Duk wanda yakawo
sauƙi ga mutumin da yake cikin tsanani, Ubangiji zai kawo masa sauƙi a duniya
da lahira. Duk wanda ya suturce Musulmi, Ubangiji zai yi masa suturta a duniya
da lahira. Lallai Ubangiji yana cikin taimakon bawa matukar bawannan ya kasance
cikin taimakon ɗan’uwansa Musulmi, wanda duk yakama tafarki yana neman ilimi a wannan
tafarki, sakamakon haka Allah zai sauwaƙe masa hanyar shiga Aljannah, babu yada
za’ayi mutane su taru a cikin wani ɗaki daga ɗakunan Allah, suna karanta
littafin Allah suna darasin littafin Allah tsakaninsu da juna, face sai natsuwa
ta sauka a kan su, sai rahama ta lullube su, sai Mala’iku sun zagaye su, sai
kuma Allah ya ambace su a fadar sa ta Mala’ikun sa. Wanda duk aikin sa yayi tsantsa
dashi baiyi gaggawa dashi ba, dangantakar sa ba za ta yi gaggawa dashi ba”.
Muslimu ne ya ruwaito shi da wannan lafazin.
0 Comments