Saurari audio na Sheikh Ja’afar Mahmud Adam
عَنْ
ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم
فِيمَا يَرْوِيهِ عَنْ رَبِّهِ تَبَارَكَ وَتَعَالَى، قَالَ: "إنَّ اللَّهَ
كَتَبَ الْحَسَنَاتِ وَالسَّيِّئَاتِ، ثُمَّ بَيَّنَ ذَلِكَ، فَمَنْ هَمَّ
بِحَسَنَةٍ فَلَمْ يَعْمَلْهَا كَتَبَهَا اللَّهُ عِنْدَهُ حَسَنَةً كَامِلَةً،
وَإِنْ هَمَّ بِهَا فَعَمِلَهَا كَتَبَهَا اللَّهُ عِنْدَهُ عَشْرَ حَسَنَاتٍ إلَى
سَبْعِمِائَةِ ضِعْفٍ إلَى أَضْعَافٍ كَثِيرَةٍ، وَإِنْ هَمَّ بِسَيِّئَةٍ فَلَمْ
يَعْمَلْهَا كَتَبَهَا اللَّهُ عِنْدَهُ حَسَنَةً كَامِلَةً، وَإِنْ هَمَّ بِهَا
فَعَمِلَهَا كَتَبَهَا اللَّهُ سَيِّئَةً وَاحِدَةً"
رَوَاهُ الْبُخَارِيُّ وَمُسْلِمٌ، في "صحيحيهما" بهذه الحروف
On the authority of Ibn Abbas (may Allah be pleased with him),
from the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him), from
what he has related from his Lord:
Verily Allah ta’ala has written down the good deeds and the evil
deeds, and then explained it (by saying): “Whosoever intended to perform a good
deed, but did not do it, then Allah writes it down with Himself as a complete
good deed. And if he intended to perform it and then did perform it, then Allah
writes it down with Himself as from ten good deeds up to seven hundred times,
up to many times multiplied. And if he intended to perform an evil deed, but
did not do it, then Allah writes it down with Himself as a complete good deed.
And if he intended it [i.e., the evil deed] and then performed it, then Allah
writes it down as one evil deed.”
(Bukhari & Muslim)
Daga ɗan Abbas Allah ya yarda da su, daga Manzon Allah (SAW) cikin
abinda yake ruwaitowa daga Ubangijinsa Mai Girma da Ɗaukaka ya ce:
“Allah ya riga ya rubuta dangogin ayyuka na al-khairi da kuma
dangogin ayyuka na ɓarna”, wanda duk ya himmatu zai aikata wani kyakkyawan aiki
sai bai samu damar aikatawa ba, duk da bai aikata ba, Allah zai rubuta masa
kyakkyawan aiki guda ɗaya, idan ya himmatu zai aikata kyakkyawan aiki, kuma ya
samu dama ya aikata wannan kyakkyawan aiki, To Ubangiji zai rubuta masa lada ɗaya
ɗaya har guda goma, za’a iya ninkawa har izuwa ga ruɓi ɗari bakwai har zuwa
sama da ɗari bakwai. In mutum ya himatu zai aikata wani mumunan aiki sai kuma
bai samu aikatawa ba, Allah zai rubuta masa hasana cikakkiya a wurinsa, idan
mutum ya himatu da mumunan aiki zai aiwatar kuma yayi wannan mumunan aiki,
Allah zai rubuta masa mumunan aiki ɗaya.
Bukhari da Muslimu ne suka ruwaito shi da waɗannan haruffa.
0 Comments