عَنْ
أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه
وسلم "إنَّ اللَّهَ تَعَالَى طَيِّبٌ لَا يَقْبَلُ إلَّا طَيِّبًا، وَإِنَّ
اللَّهَ أَمَرَ الْمُؤْمِنِينَ بِمَا أَمَرَ بِهِ الْمُرْسَلِينَ فَقَالَ
تَعَالَى: "يَا أَيُّهَا الرُّسُلُ كُلُوا مِنَ الطَّيِّبَاتِ وَاعْمَلُوا
صَالِحًا"، وَقَالَ تَعَالَى: "يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُلُوا
مِن طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ" ثُمَّ ذَكَرَ الرَّجُلَ يُطِيلُ السَّفَرَ
أَشْعَثَ أَغْبَرَ يَمُدُّ يَدَيْهِ إلَى السَّمَاءِ: يَا رَبُّ! يَا رَبُّ!
وَمَطْعَمُهُ حَرَامٌ، وَمَشْرَبُهُ حَرَامٌ، وَمَلْبَسُهُ حَرَامٌ، وَغُذِّيَ
بِالْحَرَامِ، فَأَنَّى يُسْتَجَابُ لَهُ؟
رَوَاهُ
مُسْلِمٌ
On the authority of Abu Hurayrah (ra):
The Messenger of Allah (ﷺ)
said, “Allah the Almighty is Good and accepts only that which is good. And
verily Allah has commanded the believers to do that which He has commanded the
Messengers. So the Almighty has said: “O (you) Messengers! Eat of the tayyibat [all
kinds of halal (legal) foods], and perform righteous deeds.” and the Almighty
has said: “O you who believe! Eat of the lawful things that We have provided
you.” Then he (ﷺ) mentioned (the case)
of a man who, having journeyed far, is disheveled and dusty, and who spreads
out his hands to the sky saying “O Lord! O Lord!,” while his food is haram
(unlawful), his drink is haram, his clothing is haram, and he has been
nourished with haram, so how can (his supplication) be answered?
(Muslim)
Daga Abu Hurairah Allah ya ƙara yarda a gare shi ya ce:
Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: “Lallai
Allah Ta’ala tsarkakakke ne (Kamili ne cikin siffofin sa), kuma baya karɓar abu
sai tsarkakakke. Allah ya Umarci muminai da irin abin da ya umarci Manzanni
dashi, Allah Maɗaukaki ya faɗa (Lokacin da yake umurtar Mazanni): “Ya ku
Manzanni kuci daga daɗaɗan (tsarkaka) al-amurra, kuma kuyi aiki na gari”. Allah
kuma ya faɗa (Lokacin da yake umurni ga Muminai): “Ya ku waɗanda sukayi Imani
kuci daga daɗaɗan al-amurran da muka halatta (azurta) muku su”. Sannan Annabi
(SAW) ya ambaci wani mutumin da yake tsawaita tafiya, mai gizo (gashin kansa ya
ƙuƙƙulle) mai ƙura, yana miƙa hannayensa biyu zuwa ga sama, ya Ubangiji ya
Ubangiji, abincinsa haramunne, abin shansa haramunne, tufafinsa haramunne, an
ciyar dashi haramun tun yana yaro, ta yaya za’a amsa masa addu’ar sa?”.
0 Comments